Jamus na so a binciki kamfanin Volkswagen | Labarai | DW | 22.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus na so a binciki kamfanin Volkswagen

Ma'aikatar sufurin ƙasar Italiya bayan da aka bankado zamba a inijnan motocin Volkswagen a Amirka ta ce ita ma a yi bincike a motocin kamfanin da ke kasar.

USA Volkswagen Michael Horn

Michael Horn na kamfanin Volkswagen

Ma'aikatar sufuri a ƙasar Italiya ta bayyana a ranar Talatan nan cewar ta bude gudanar da bincike kan aikata zamba kan batun abin da injininan motocin da kamfanin Volkswagen da ya zama fitacce wajen kera motoci irinsu Golf da Passat da Audi a Jamus ke fitarwa na iskar Carbon, inda ta bukaci wannan kamfani ya ba ta bayanai.

A cewar ma'aikatar sufurin kasar ta Italiya ta damu matuka da jin labarin zamba da aka bankado a kasar Amirka inda aka gano cewa cikin injinin motoci da ke amfani da man diesel da kamfanin ke kerawa an gano cewa akwai wata na'ura da kan bada bayanai marasa inganci kan iskar ta Carbon da motocin ke fitarwa, dan haka zasu gudanar da bincike ko a kasashen na Turai ma haka abin yake.

Tuni dai ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmier ya bayyana fatan ganin an gudanar da binciken dan tabbatar da sahihancin zargin da ake wa motocin na Volkswagen.

Ya ce "Ina fatan za a gudanar da bincike nan ba da dadewa ba, cikin gaggawa dan gano yadda aka gudanar da wannan almundahna da ake zargi, musamman a gano mutanen da ke da hannu wajen aikata haka, dole agudanar da wannan bincike dan kare martabar kamfanin na Volkswagen, sannan nan gaba mu gana kan wannan batu tsakanin kamfanin da mahukuntan na Amirka dan gano yadda aka kai ga wannan mataki".