1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na iya bai wa Edward Snowden mafaka ?

November 4, 2013

Snowden ya ce a shirye yake ya zo Jamus a yi masa Tambayoyi don ba da ƙarin haske a kan satar bayanan sirri da hukumar leƙen asirin Amirka ta riƙa yi wa Angela Merkel.

https://p.dw.com/p/1ABE1
German Greens lawmaker Hans-Christian Stroebele poses for a picture with fugitive former U.S. spy agency contractor Edward Snowden (L) in an undisclosed location in Moscow, October 31, 2013. Stroebele met Snowden in Moscow on Thursday, Stroebele's office said in a statement, and would give details of the meeting on Friday. Snowden passed on an envelope with a letter addressed to the German government, Germany's lower house of parliament, the Bundestag, and to the Federal Public Prosecutor (Generalbundesanwalt). The letter is to be disclosed during a news conference on Friday in Berlin. REUTERS/Handout (RUSSIA - Tags: POLITICS TPX IMAGES OF THE DAY) ATTENTION EDITORS � THIS IMAGE WAS PROVIDED BY A THIRD PARTY. NO SALES. NO ARCHIVES. FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS PICTURE IS DISTRIBUTED EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hans-Christian Ströbele ɗan majalisar dokokin Jamus tare da Edward SnowdenHoto: Reuters

Rawuwar Edward Snowden tsohon jami'in leƙen asirin na Amirka wanda yanzu haka ya sami mafaka ta siyasa a Rasha,ta kasance a cikin kewa ta rashin 'yan uwa da dangi da kuma sauran wasu abubuwa na rayuwa.To sai dai kuma ana hasashen cewar watakila Jamus ta kan yiyuwa ta ba shi mafakar siyasar, batun da kuma 'yan siyasa na Jamus ɗin suke ta yin tsokaci akai.

Abu ne mai yiwuwa a cewar wata yar Siyasar ta jam'iyyar masu kare muhalli

Wannan tunani dai ya biyo bayan ziyarar da wani ɗan siyasar ɗan majalisa na jam'iyyar masu fafutukar kare muhalli Hans Christian Ströbele ya kai wa Snowden ɗin a birnin Moscow inda ya gana da shi kana kuma suka tattauna, wanda a kan haka ake ganin a kwai buƙatar Snowden ɗin ya iso a Jamus kamar yadda yayi fata, domin ya bayyana a gaban wani kwamiti na musamman don ba da ƙarin haske a kan zargin da ake yi wa hukumar NSA da tatsar bayanan sirri na wayar salula ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, kafin daga bisani shi ma ministan cikin gida na ƙasar ta Jamus Hans-Peter Friedrich,ya ce a shirye suke su saurari tsohon jami'in na Amirka indan har ya zo. Abin dai yana da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, domin idan har Snowden ɗin ya kuskura ya yi balaguron to kam zai iya rasa matsayin da yake da shi na ɗan gudun hijira a Rasha. Sai dai kuma wani ofishin bincike na majalisar dokokin ta Jamus ɗin wato Bundestag ya ce ana iya a gewaye yarjejeniyar da ke tsakanin Amirka da ƙasashen Kungiyar Tarayyar Turai, na tisa ƙeyar masu laifin zuwa ƙasashen. Abin da kuma mataimakiyar shugaban majalisar dokokin Claudia Roth ta ce yana yiwuwa a aikata shi a kan Snowden :'' A gare mu sigina ce mai kyau Edward Snowden ya iso Jamus zai kasance shaida a gaban kwamitin binciken, wanda muke yin fafutuka a kansa.''

Die Grünen-Chefin Claudia Roth spricht am 27.04.2013 auf der Bundesdelegiertenversammlung zu den Delegierten. Drei Tage lang beraten die Delegierten von Bündnis 90/Die Grünen über ihr Programm für die Bundestagswahl im Herbst. Foto: Ole Spata/dpa
Claudia Roth mataimakiyar shugaban majalisar dokokin JamusHoto: picture-alliance/dpa

Martanin ɓangaren gwamnatin a kan wannan danbarwar

A wani binciken da ta gudanar wata jarida ta nan Jamus Der Spiegel, ta ce kusan kashi 50 cikin 100 na al'ummar ta Jamus na buƙatar Snowden ɗin ya iso a Jamus don a yi masa tambayoyi Bernd Riexinger na jam'iyyar Linke na daga cikin waɗanda ke da írin wannan ra'ayi.Ya ce :''Snowden ya taimaka ga samin haske ga abin da hukumar leƙen asirin Amirka ta ke yi na satar wayoyin jama'a da shugabannin ko China ko Rasha ko wacce ƙasa ma ya kamata ta ba shi mafakar siyasa.'A yanzu shugabar gwamatin Jamus Angela Merkel ba ta ce komai ba dangane da wannan batun na ba da mafakar siyasar, to amma wani darakta a fadarta Michael Grosse Brömer ya mayar da martani, inda ya ce : ''Babu wata bita da ƙuli ta siyasa da ake yi masa kuma wannan buƙata ba ta cikin dokar kwamitin na iya zuwa Rasha domin sauraron Snowden ɗin''

ARCHIV - Der niedersächsische CDU-Bundestagsabgeordnete Michael Grosse-Brömer lächelt am 21.05.2012 in Berlin. Die drohende Altersarmut muss nach Ansicht von Grosse-Brömer in einem großen gesellschaftlichen Schulterschluss bekämpft werden. Foto: Soeren Stache dpa
Michael Grosse-Brömer wani ɗan jam'iyyar CDU na kusa da Angela MerkelHoto: picture-alliance/dpa

Mawallafi :Taube Friedel/Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe