Jamus: Merkel ta sake fuskantar karkarwar jiki | Labarai | DW | 10.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Merkel ta sake fuskantar karkarwar jiki

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sake fuskantar matsalar zanzana ko karkarwar jiki a karo na uku a bainar jama'a yayin da ta ke ganawa da Firaministan kasar Finland Antti Rinne a wannan Laraba a birnin Berlin.

Saidai da take bayani a gaban 'yan jarida tare da Firaministan kasar ta Finland,  Merkel ta ce tana cikin koshin lafiya. Sai dai ta ce ana yi mata bincike kan wannan matsala tata.

A ranar 18 ga Yunin da ya gabata ne Merkel da ke shirin cika shekaru 65 a ranar Laraba mai zuwa, ta fara fuskantar a karon farko wannan larura ta karkarwar jiki a lokacin da ta karbi bakuncin Shugaban Kasar Ukrain Volodymyr Zelenskiy a birnin Berlin, kafin matsalar ta sake dawo mata a ranar 27 ga watan na Yuni lokacin wata ganawa da shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier awoyi kalilan kafi tashi zuwa taron koli na G20 a kasar Japan.