1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daba wa 'yar siyasa wuka ya sa ta ci zabe a Jamus

Muhammadou Auwal Balarabe/YBOctober 19, 2015

Henriette Reker ta lashe zaben magajin gari a Köln, a daidai lokacin da kungiyar Pegida da ke Allah wadai da shigowar Musulmi ke cika shekara da babbar zanga-zangarta a Dresden.

https://p.dw.com/p/1GqSk
Köln Oberbürgermeisterwahl Kandidatin Henriette Reker
Henriette Reker 'yar siyasa da aka daba mata wukaHoto: picture-alliance/dpa/O. Berg

Kashi 4% na kuri'un da aka kada a zaben kananan hukumomi na Köln ne Jam'iyyar da ke kyamar baki a Jamus wato Alternative für Deutschland ta samu. Amma kuma duk da haka manufofinta na ci gaba da haddasa kace-nace sakamakon niyar hallaka daya daga cikin 'yan takara da wani mai wannan akida ya yi gabanin wannan zabe. Duk da cewa har yanzu ta na kwance a asibiti, amma kuma wannan yunkuri ya zamewa Henriette Reker gobarar Titi, saboda an zabeta a mukamin magajin gari tun a zagayen farko alhali kuwa ba ta tsaya a karkashin wata jam'iyya ba.

Dama dai madame Reker ce ke kula da harkokin da suka shafi sajewar baki a birnin na Köln da ya kunshi dimbin baki ciki kuwa har da Musulmi. Lamarin da wanda ya yi niyar kaita lahira ya danganta da wata dama ta yada shari'ar Musulunci a Jamus tare da bai wa baki damar mamaye gurabensu na aiki.

Sai dai kuma Marlies Bredehorst, shugabar reshen jam'iyyar The Greens da ke da rajin kare muhalli a Köln, ta ce zaben Henriette Reker a mukamin magajin gari ya nunar da cewar birnin na Allah wadai da duk wasu al'amura da suka shafi kyamar baki.

"Ina ganin cewar bayan wannan danyen aikin da aka fuskanta, birnin Köln na bukatar canjin kamun ludayi. Imma a fannin tsarin sufuri ko al'adu da hallaya da sauransu, ya kyautu a dora shi a kan wani sabon babi. Henriette ce za ta iya kawo wannan sauyi."

Köln Messerattacke auf OB-Spitzenkandidatin Reker Solidaritätskundgebung Menschenkette
'Yan siyasa da ke goyon bayan Henriette Reker da aka dabawa wukaHoto: picture-alliance/dpa/O. Berg

Sai dai kuma Jamusawa da yawa sun canja ra'ayinsu kan batun tarbar 'yan gudun hijirar Syriya da Iraki, inda a yanzu fiye da rabin 'yan kasar ke adawa da manufofin gwamnati na bude kofofi ga wadanda ke gudun yaki a kasashensu. Alalhakika ma dai hare-hare kan bakin da ke neman mafaka sun karu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Sannan kuma kotun da ke kare tsarin mulkin Jamus ta yi gargadin cewar hare-hare kan baki za su iya karuwa nan gaba sakamakon karuwar kyamar baki.

A yanzu haka dai kungiyar nan da ke da manufar nuna wariya ga baki wato Pegida ta sake shiga kanun labarai, inda dubban magoya bayanta suke shirin gudanar da gangami a birnin Dresden domin kalubalantar manufofin gwamnati. Wannan ya zo ne shekara guda cif da kaddamar da wannan kungiya, lamarin da ke bakanta ran ministan Jamus da ke kula da harkokin cikin gida Thomas de Maiziere. saboda hake ne ya yi kira ga al'umma da su nesanta kansu daga manufin wannan kungiya.

Köln Messerattacke auf OB-Spitzenkandidatin Henriette Reker
Jami'an lafiya a lokacin kai dauki ga wadanda harin daba wuka ya shafa a KölnHoto: picture-alliance/ANC ESSEN/dpa

"Abin lura a nan shi ne kotun kare kundin tsarin mulki na sa ido sosai a kan Pegida. Ta fara ne tun bayan da aka fara tafka mahawara kan ko wannan kungiya na da manufofin kyamar baki koko a'a, lamarin da ya fito fili. Mambobinta na shirya zanga-zanga domin nuna cewar masu neman mafaka ba su da mutunci, 'yan siyasan Jamus kuma munafukai ne. Har yanzu dai ba a cimma matsaya a kan wannan batu ba. Duk wanda ya nuna damuwa kan abubuwan da suke fada ya na basu hadin kai ne."