Jamus: Kotu ta karya shari′ar Salafawa da aka saki | Labarai | DW | 11.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Kotu ta karya shari'ar Salafawa da aka saki

Babbar kotun kasar Jamus ta karya hukuncin da kotun birnin Wuppertal na tsakiyar kasar ta yanke na sakin wasu Salafawa bakwai da aka samu da laifin girka rundunar 'yan sanda Sharia'ar Muslunci ta bayan fage.

Babbar kotun kasar Jamus ta karya a wannan Alhamis hukuncin da kotun birnin Wuppertal ta dauka a shekara ta 2016 na sakin wasu Salafawa bakwai da aka samu da laifin girka rundunar 'yan sanda ta bayan fage da ke kula da harakokin shari'ar Muslunci a tsakanin al'ummar Musulmi mazauna garin Wuppertal na tsakiyar kasar. 

Babbar kotun kasar ta Jamus ta ce kotun ta birnin Wuppertal ta yi babban kuskure wajen yanke hukuncin nata. A zaman da ta yi a shekarar ta 2016 kotun birnin na Wuppertal ta saki mutanen ne a bisa hujjar cewa saka kayan kaki da suka yi bai saba wa dokokin kasar ta Jamus ba.  

A watan Satumban 2014 ne aka samu Salafawan guda bakwai sanye da kayan kaki wadanda aka rubuta "Yan sandar Chari'a" a samansu suna gudanar da sintiri a saman titunan birnin na Wuppertal mai kunshe da Muslmi da dama, inda suke tare matasan Musulmi suna gargadinsu kan su kaurace wa shan barasa da zuwa gidajen rawa da na wasanni da na caca.