An yi hasashen cewar Jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya ta Angela Merkel CDU na kan gaba a zaben 'yan majalisu na jiha da aka gudanar a Jihar Sachsen Anhalt da ke a kudu maso gabashin Jamus
Hasashen ya nuna cewar jam'iyyar CDU ta samu kishi 35 zuwa 36 na kuri'u da aka kada, yayin da jam'iyyar da suke hamayya da ita, ta masu kaymar baki AFD ta samu kishi 22 zuwa 23. Wannan zabe dai na wannan jiha da ke cikin tsohuwar Jamus ta Gabas na zaman zakaran gwajin dafi kana na karshe kafin zaben kasa da za a yi a cikin watan Satumba da ke tafe.