Jamus: Gano sabbin cibiyoyin gwale-gwale na boye | Labarai | DW | 16.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Gano sabbin cibiyoyin gwale-gwale na boye

Wata kungiyar fafutika a Jamus ta gabatar da wani shafin intanet da ta bude wanda ya kunshi sabbin cibiyoyin gwale-gwale na 'yan Nazi na boye da ta gano a wani aikin bincike da ta gudanar.

A kasar Jamus an gabatar a wannan Alhamis da wani shafin Intanet na musamman wanda ya kunshi wasu sabbin bayanai da aka tattara a loakcin wani aikin bincike da wata kungiyar fafutika ta gudanar na neman gano sauran kankanan gidajen gwale-gwale na 'yan Nazi wadanda suka yi aiki kafada da kafada da babban sansanin gwale-gwale na Auschwitz wanda gwamnatin 'yan Nazi ta gina a lokacin yakin duniyan na biyu.

 A wani taron manema labarai da ta gudanar a wannan Alhamis a birnin Berlin inda ta gabatar da sakamakon aikin nata, kungiyar fafutikar mai suna Tiergartenstraße 4 Association ta ce shafin nata na intanet ya kunshi sakamakon ayyukan binciken ta share shekaru tana yi wanda ya ba ta damar gano wasu kananan sansanonin gwale-gwalen na boye kimanin 45 a wasu wurare na kewaye da babban sansanin na Auschwitz.

 Sabon shafin kungiyar ya kunshi hotuna sama da dubu uku da 500 da kuma tasawirori wadanda ke nuna tarihin gidajen gwale-gwalen da sunayen 'yan kasan da suka tsira da ransu, irin azabar da aka dunga yi masu da sunanen jami'an rundunar 'yan sanda ta musamman da aka fi sani da suna SS da ke tsaron gidajen.