Jamus: Fargabar yiwuwar sake bullar Covid-19 | Labarai | DW | 16.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Fargabar yiwuwar sake bullar Covid-19

Bisa ga wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi a Jamus, akwai shirin daukar tsauraran matakai na hana zirga-zirga domin dakile yaduwar cutar Covid 19 saboda fargabar barkewar cutar a karo na biyu.

Daga cikin sabbin dokokin, za a hana shiga da fice daga duk yankunan da aka sami karuwar cutar. Ana sa ran cimma matsayan karshe kan wannan mataki a wannan rana ta Alhamis.

Jamus da ta sami saukin annobar idan an kwatantata da sauran makwabtanta, ba ta son cutar tai mata zuwan bazata a wannan karon wanda hakan ya sa suka yanke shawarar daukan matakai tun da wuri.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a ranar talatar da ta gabata ta nuna goyon bayanta ga wannan mataki.