1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rigakafin kyanda ya zama dole a Jamus

Abdullahi Tanko Bala
November 14, 2019

Daga watan Maris na 2020 dole iyaye su nuna takardar shaidar an yi wa 'ya'yansu allurar rigakafin kyanda kafin a amince su shiga makaranta

https://p.dw.com/p/3T3n6
Masernwelle in Deutschland
Hoto: Getty Images/S. Gallup

Majalisar wakilan Jamus ta amince da dokar da za ta tilasta yi wa kananan yara allurar rigakafin kyanda.

Dokar za ta fara aiki ne daga ranar daya ga watan Maris na shekarar 2020.

'Yan majalisa 459 suka kada kuri'ar amincewa da dokar yayin da 89 suka ki amincewa 'yan majalisar 105 kuma suka kaurace.

Dokar dai za ta bukaci iyaye su nuna shaidar an yiwa 'ya'yansu rigakin kafin a karbe su shiga makaranta.

Iyayen da suka ki kai 'ya'yansu rigakafin na iya fuskantar tara ta kimanin euro 2,500

Ministan lafiya Jens Spahn yace kare yara daga cutar kyanda hakki ne na yaran.

Dokar za ta yi aiki akan dukkan jama'a har da masu neman mafakar siyasa a Jamus.