1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Jamus ta kafa dokar kare muhalli

Abdoulaye Mamane Amadou
December 20, 2019

Gwamnatin Taryyar Jamus ta samar da wata doka da ke fayyace irin tsarin da kasar ta tanada wajen kare muhalli wanda majalisar dokokiMajalisar dokokin kasar ta yi na'am da ita.

https://p.dw.com/p/3V9BD
BdW Global Ideas Bild der Woche KW 36/2016 Deutschland Braunkohlekraftwerk
Hoto: picture-alliance/ZB/P. Pleul

Dokar da ke a matsayin wani gagarumin yunkuri na kawancen jam'iyyun da ke mulkin kasar na zuwa ne, biyo bayan abinda masu sharhi ke ganin cewa akwai yiwuwar fuskantar matsin lamba na cikin gida a tsakankanin jam'iyyun da ke kawancen masu mulki, musamman jam'iyyar nan mai fafatikar kare muhalli ta GREEN, baya ga wasu tarin masu zanga zanga da ke neman ganin gwamnatin ta yi wani abu a zahiri kan batun na fitar da hayaki mai gurbata muhalli.

Tun a gabanin jefa kur'ar na'am da wannan dokar da majalisar dokokin kasar ta yi, majalisar ta yi wata ganawa da bangarorinta da dama tare da shawarwarin bullo da wasu sababbin matakai ciki har da bayar da tallafi ga kamfanonin kera motoci masu amfani da wutar lantarki, hakan da samar da wata kasuwa ta sayar da sanadari Carbone zalla zuwa shekarar 2021.