Harin bindiga a birnin Halle na Jamus
October 9, 2019Talla
Bikin ranar ta Yom Kippur dai na zaman mafi mahimmanci a shekara ga Yahudawan, inda su ke azumi don neman gafara. Maharin dai ya tsere wanda hakan yasa jami'an 'yan sanda suka umurci mutane da su zauna a gida wadanda ke kan hanya kuma su nemi wajen da za su boye kansu.
A wata sanarwar da suka fitar a shafinsu na Twitter, jami'an 'yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutanen da kuma tserewar dan bindigar da wata mota, sai dai sun ce sun yi nasarar cafke wani mutum guda da su ke zargin sa da hannu a harin. Yanzu haka dai ma'aikatar lura da zriga-zirgar jiragen kasa da ke garin na Halle ta sanar da dakatar da aiki.