1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Italiya za su fada matsalar tattalin arziki

October 11, 2022

Asusun bada lamuni na IMF ya yi hasashen cewa kasashen Jamus da Italiya za su fada matsalar koma bayan tattalin arziki a 2023

https://p.dw.com/p/4I3dh
Berlin-Mitte, Zentrum vom Fernsehturm - -
Hoto: akg-images/picture-alliance

Idan hasashen ya tabbata to wannan zai kasance karon farko da kasashen biyu da ke cikin kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya za su fada matsalar tattalin arziki tun bayan da Rasha ta kaddamar da hare hare a kan Ukraine.

A nazarin tattalin arzikin duniya da ya yi, asusun yace tattalin arzikin Jamus zai ragu da digo uku cikin dari a 2023 sabanin cigaban da yace tattalin arzikin zai da digo takwas cikin dari.

Jamus kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Turai ta dogara ne sosai a kan makamashin gas daga Rasha wanda Moscow ta dakatar a matakin ramuwar gayya ga takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata.