1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Israila sun farfado da zumuntarsu

Abdullahi Tanko Bala
October 4, 2018

Jamus da Israila sun farfado da tattaunawar zumunta a tsakaninsu bayan rashin jituwa tsawon lokaci kan batun fadada matsugunan Yahudawa.

https://p.dw.com/p/3606m
Deutschland Benjamin Netanjahu, Premierminister Israel & Angela Merkel in Berlin
Hoto: Reuters/A. Schmidt

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kai ziyara Israila mako guda bayan da Firaministar Israilar Benjamin Netanyahu ya zargi shugabannin Turai da kare masu mulkin kama karya na kasar Iran.

Shugabannin biyu na shirin farfado da tattaunawa akai akai tsakanin kasashensu wanda aka dakatar a bara bayan da Merkel ta ki amincewa da shirin Israilar na fadada matsugunan Yahudawa a yankin gabar yamma.

Jamus da wasu kasashen Turai dai sun sha sukar Israila kan shirinta na fadada matsugunai a yankin Falasdinawa tare da gargadi, ta kiyayi wargaza fatar masalahar da ake so a cimma na samar da kasashe biyu tare da Falasdinawa da za su zauna daura da juna.

Shugaba Angela Merkel ta kuma baiyana cewa ita da Firaminista Benjamin Netanyahu sun jingine banbance banbancen da ke tsakaninsu za kuma su karfafa hadin kai a tsakanin kasashen.

Ta yi alkawarin cewa Jamus za ta ci gaba da adawa da akidar nuna wa Yahudawa kyama.