1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Frank-Walter Steinmeier ya je Halle

Zulaiha Abubakar
October 10, 2019

Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bukaci hadin kai tsakanin al'ummar Jamusawa bayan harin da ya kashe mutane biyu a garin Halle da ke gabashin kasarranar Laraba.

https://p.dw.com/p/3R46W
Deutschland Halle nach Anschlag auf Synagoge | Frank-Walter Steinmeier, Bundespräsident
Frank-Walter Steinmeier ya je gaisuwa Halle, bayan harin kan YahudawaHoto: Reuters/H. Hanschke

Duk da cewar maharin bai samu nasarar kutsawa wurin ibadar Yahudawan ba, ya cimma harbe mutane biyu da ke kan titi. Ya dai yada wani faifayen bidiyo da ya dauka kai tsaye ta shafukan sada zumunta. Mummunan al'amarin dai ya yi kama da harin da ya faru a New Zealand a shekarar bara.

Majiyar dakarun sojoji na nuni da cewar, wanda ake zargi da kai harin mai suna Stephan B. kuma Bajamushe, ya yi aki a rundunar sojojin, sai dai bai samu wani horo na musamman ba. Rahotanni sun nunar da cewa bayan mutane biyun da suka rasa rayukansu, wasu mutane biyu kuma sun samu rmunanan raunuka.