Jamus: Baki dubu 30 sun bace | Labarai | DW | 02.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Baki dubu 30 sun bace

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na fuskantar matsin lamba kan bacewar wasu 'yan kasar waje dubu 30, wadanda aka hanasu izinin samun mafakar siyasa a cikin kasar.

Jaridar Bild da ke fitowa a kowace rana ta ce, jam'iyyun da ke shirin kafa gwamnatin hadaka da Merkel na matsin lambar amincewa da yarjejeniyar da zata kaucewa sake aukuwar matsalar kwararowar baki zuwa cikin kasar kamar na shekara ta 2015.

Jaridar ta cigaba da cewar, bakin na cikin mutanen da ya kamata su fice daga kasar tun watan Disamba 2016, bayan watsi da takardunsu na neman izinin zama. Sai dai watakila wasunsu, sun bar kasar ba tare da sanin hukumomi ba. 

Masu zabe a nan Jamus sun gasawa shugabar gwamnati tsakuwa a hannu lokacin zaben watan Satumba, inda jam'iyyarta na masu ra'ayin mazan jiya ta yi asarar kujerunta ga jam'iyar masu ra'ayin kyamar baki ta AFD.