Jamus: Badakalar gwajin hayakin Diesel kan mutane | Labarai | DW | 30.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Badakalar gwajin hayakin Diesel kan mutane

A Jamus an bankado wata sabuwar badakala kan yadda wasu kamfanonin kera motoci na kasar suka yi amfani da birrai da ma 'yan Adam wajen yin gwajin illar da gurbataccen hayakin da injinan Diesel ke yi kan halittu. 

 

Jaridar Stuttgarter Zeitung da ta Süddeutsche ne suka bayyana wannan labari a jiya Litinin inda suka ce an gudanar da gwajin ne a shekara ta 2013 da ta 2014 a kan wasu mutane 25 masu koshin lafiya da aka shaka masu hayakin na Diesel da nufin fahimtar yadda yake shafar lafiyar dan Adam.

A wani taron manema da ya kira a jiya Litinin kakakin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wato Steffen Seibert ya ce ba bu wata hujja ta gudanar da wannan gwaji wanda ya ce ya saba wa ka'ida.

Kakakin shugabar gwamnatin ta Jamus ya bayyana cewa za a gayyaci kamfanonin kera motocin a gaban kwamitin da ke bincike kan badakalar injinan Diesel  tare da ba su umurnin dakatar nan take da wannan gwaji.