Jamus: An yi wa sama da miliyan daya rigakafi a rana daya | Labarai | DW | 29.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: An yi wa sama da miliyan daya rigakafi a rana daya

A wani abin da ake maraba da shi bayan kwashe tsawon lokaci batun rigakafin corona na tafiyar hawainiya, ma'aikatar lafiya a Jamus ta fidda sanarwar yi wa sama da mutum miliyan guda allurar rigakafi corona a rana guda.

Ana ganin cewa wannan gangamin rigakafin ya kara yawan wadanda suka sami allurar a nahiyar Turai a cewar Jens Spahn da ke zama ministan lafiya a Jamus.

Ya ce wannan mataki ya nuna irin hanzarin da za su iya cimma wa a cikin kankanin lokaci. Baya ga kasashen China da Amirka da Indiya babu wata kasa da ta yi yawan allurar da Jamus din ta yi a ranar Laraba ba.

Birtaniya ta kwatanta inda a cikin sa'o'i 24 ta yi wa sama da mutum dubu dari takwas rigakafin.

Yanzu dai sama da kashi 25 cikin 100 na al'umma a Jamus sun karbi kason farko na rigakafin yayin da dama daga cikinsu sun kammala duka.