1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan bingiga ya budewa wasu mutane wuta a Jamus

Zulaiha Abubakar
February 20, 2020

Yan sandan Jamus sun bayyana mutuwar mutumin da ake zargi da harbin wasu mutane a birnin Hanau cikin wata sanarwa da hukumar tsaro ta wallafa a shafinta na twitter.

https://p.dw.com/p/3Y2Kj
Deutschland Tote durch Schüsse in Hanau
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Probst

A daren Jiya Laraba ne dan bindigar ya budewa wasu mutane wuta yayinda suke tsaka da shan shayi a wasu shaguna biyu da ke Kudu maso Yammacin Jamus, almarin dai yayi sanadiyyar mutuwar mutane tara bayan wasu mutanen biyar sun samu munanan raunuka. Binciken gaggawar da jami'an tsaron suka gudanar ya nunar da yadda wata mota tayi saurin arcewa daga shagon farko da al'amarin ya afku mintuna kalilan.

Jami'an 'yan sandan na Jamus dai na ci gaba da gudanar da bincike a birnin na Hanau na jihar Hesse da ke da yawan mutane kimanin dubu dari.