1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama yan fashin gidan tarihi na Dresden

Abdullahi Tanko Bala
November 17, 2020

Rundunar 'yan sandan jamus a birnin Berlin sun kama mutane uku wadanda ake zargi da hannu a satar kayayyaki masu daraja a wani gidan adana kayan tarihi dake gabashin birnin Dresden a 2019.

https://p.dw.com/p/3lQT1
Einbruch Grünes Gewölbe Dresden
Hoto: picture-alliance/dpa/ZB/S. Kahnert

Mutanen uku da aka kama dukkaninsu Jamusawa ne. Masu gabatar da kara sun ce sun yi imani wadanda aka kama din suna da hannu a fashin.

'Yan fashin sun balla gidan tarihin ne a ranar 25 ga watan Nuwamban 2019 inda cikin 'yan mintuna kalilan suka sace gwala-gwalai masu daraja na kasrni na 18 suka kuma tsere a cikin mota.

An yi nasarar kamen bayan wani gagarumin farmaki a wurare goma sha takwas wanda ya kunshi 'yan sanda fiye da 1,600 a fadin Jamus.

'Yan sandan sun ce har yanzu suna cigaba da neman wasu mutane biyu ruwa a jallo da ake zargi sum a suna da hannu a satar.