Jam′iyyu a majalisar dokokin Jamus sun yi tir da razana ′yan gudun hijira a Saxony | Labarai | DW | 24.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyu a majalisar dokokin Jamus sun yi tir da razana 'yan gudun hijira a Saxony

An zargi hukumomin tsaro da gazawa wajen ba da cikakkiyar kariya ga 'yan gudun hijirar da suka shiga cikin fargaba.

Jam'iyyu da ke da wakilici a majalisar dokokin Jamus sun yi tir da wani lamari na kyamar baki da ya auku a jihar Saxony da ke gabashin kasar. Günter Krings da ke zama sakataren majalisar a ma'aikatar cikin gida ya ce sun kadu matuka da lamarin da ya auku a garuruwan Clausnitz da Bautzen. Jam'iyyar masu ra'ayin sauyi ta Linke cewa ta yi wajibi ne demokradiyya ta ci gaba da wanzuwa a yankin. Ita kuwa jam'iyyar The Greens ta zargi hukumomin tsaro ne da gazawa, sannan ta soki lamirin shugabar gwamnati Angela Merkel da sauran ministoci da suka kaurace wa zaman muhawarar kan batun. A karshen makon da ya gabata dai wani gungun mutane sun hana wata bas dauke da 'yan gudun hijira sauke mutanen da ta dauko a garin Clausnitz yayin da garin Bautzen kuma wasu 'yan kallo suka yi ta murna lokacin da aka cunna wa wani otel wuta da ake shirin sauke 'yan gudun hijira ciki.