1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alex Titto na LP ya lashe zaben Abia

Zainab Mohammed Abubakar
March 22, 2023

Dan takarar kujerar gwamna a karkashin inuwar jam'iyyar Labour Alex Titto ya lashe zaben jihar Abia da ke kudancin Najeriya.

https://p.dw.com/p/4P5jn
Shugaban jam'iyar Labour Peter Obi
Shugaban jam'iyar Labour Peter ObiHoto: Patrick Meinhardt/AFP

Alex Titto shi ne dan takarar gwamna na farko da ke samun nasara a karkashin jam'iyyar ta Labour da dan takararta Peter Obi ya zo na uku a zaben shugaban kasar na 2023.

Jam'iyyar ta Labour dai, ta yi nasarar kwace mulkin ne daga hannun PDP da gwamna Okezie Victor Ikpeazu ya shafe wa'adin mulki biyu, yanzu dai ana ci gaba da dakon sakamakon zaben gwamnan jihar Enugu.

Zanga-zanga ta barke a jihohin yankin Kudu maso Gabashin Najeriyar a tsawon lokacin da aka kwashe ana jiran hukumar zabe ta fitar da sakamakon da kowanne bangare ke zargin juna da yunkurin sauya sakamakon zaben na gwamnoni.