Jagorar jam′iyyar AfD ba ta da niyyar shiga zabe | Labarai | DW | 19.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jagorar jam'iyyar AfD ba ta da niyyar shiga zabe

A karshen mako ne dai jam'iyyar mai adawa da baki za ta yi babban taro inda anan ne za ta zayyana 'yan takara da za su jagoranci jam'iyyar ta AfD a kokari na danganawa majalisar dokokin Jamus.

Frauke Petry, jagorar jam'iyyar masu adawa da baki ta AfD  ta bayyana a ranar Laraban nan cewa ba za ta jagoranci yakin neman zaben jam'iyyar ba a zaben ranar 24 ga watan Satimba.

A jawabin da ta fitar na bidiyo a shafinta na Facebook ta yi jawabi kamar haka:

"A kokari na kawo karshen duk wani cece-ku-ce  na yi wannan hoton bidiyo inda na ke cewa babu wani tsari daga bangarena na jagorantar jam'iyyar a matsayin 'yar takara ko shiga a dama da ni a neman wata babbar kujerar shugabanci".

A karshen mako ne dai jam'iyyar za ta yi babban taro inda anan ne za ta zayyana 'yan takara da za su jagoranci jam'iyyar ta AfD a kokari na danganawa majalisar dokokin Jamus a karon farko.