1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila za ta gana da Rasha kan Iran

Abdoulaye Mamane Amadou
February 5, 2019

Kasar Isra'ila ta zafafa ruwan bama-bamai da harba rokoki ga sansanonin sojan Iran a Siriya, bisa zargin cewar Iran, na tallafa wa mayakan Hezbollah a kasar Lebanon.

https://p.dw.com/p/3CmMZ
Russland Benjamin Netanjahu, Premierminister Israel & Wladimir Putin
Hoto: Reuters/Y. Kadobniv

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewar zai gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin dangance da batun girke sojojin Iran a kasar Siriya. An bayyana cewar shugabannin biyu za su yi ganawar ne a ranar 21 ga wannan watan a birnin Moscow wanda hakan ke a matsayin irinsa na farko tun bayan da kasar Isra'ila ta bayyana kai wasu farmaki ga rundunar sojan Iran mai samun goyon bayan kasar Rasha a kasar Siriya.

Kasar Isra'ila ta zafafa ruwan bama-bamai da harba rokoki ga sansanonin sojan Iran a Siriya, bisa zargin cewar Iran, na tallafa wa mayakan Hezbollah a kasar Lebanon.

Hukumomin Moscow da Tehran na dasawa da gwamnatin Bashar al-Assad, inda suke ba shi tallafin soja da na makamai, don kawar da mayakan tawaye da kungiyoyin 'yan jahadi.