Isra'ila da Hamas sun amince su tsagaita wuta a Gaza
October 9, 2025
Isra'ila da Hamas sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza a wannan Alhamis a karkashi tsarin shugaban Amurka Donald Trump, abin zai ba da damar sakin mutanen da kungiyar ta yi garkuwa da su a lokacin harin ranar bakwai ga watan Oktoban 2023.
Wannan na zama wani babban mataki da bangarorin biyu suka cimma domin kawo karshen yakin shekaru biyu da aka kwashe ana fafatawa a yankin Falasdinu wanda ya yi ajalin rayuka da dama.
Majiyoyi da dama sun ruwaito cewa bangarorin biyu za su rattaba hannu kan wannan yarjejeniya a wannan Alhamis a Masar, sai dai har kawo wannan lokaci ba a sanar da lokacin da za ta fara aiki ba, yayin da hukumar kare fararen hula ta Gaza ta ce Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a yakin.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netenyahu ya ce zai zauna da majalisar ministocinsa a yau domin tabbar musu da sharuddan yarjeniyar, yayin da shugaban Amurka Donald Trump ya jinjinawa dukannin bangarorin kan wannan mataki da aka kai.
A cikin wani sako da ta wallafa a shafin X rundunar sojin ta Isra'ila ta ce ta yi maraba da yarjejeniyar kuma tuni ta fara shirye-shiryen karbo Isra'ilawan da suka shafe shekaru biyu a hannu Hamas, sannan kuma ta kara da cewa ta yi shiri domin tunkarar duk wani abin da ka iya biyo baya tare da umurtar mazauna Gaza da kadda su koma arewacin yankin inda ta ke ci gaba ta kai hare-hare.
A cewar wata majiya mai kusanci da Hamas za a yi musayar Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su akalla 20 daga cikin 47 a lokaci guda da fursunoni Falasdinu kusan 2,000, kuma Isra'ila ta gabatar da taswirar farko dangane da fara janye sojojinta daga dan karamin yankin na Falasdinu.