Iran ta yi kira da a dakatar da matakan soji a Yemen nan-take | Labarai | DW | 26.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta yi kira da a dakatar da matakan soji a Yemen nan-take

Saudiyya ce ke jagorantar taron dangin da kasashen Larabawa suka yi wa mayakan Huthi da suka lashi takobin kifar da shugaba Mansour Hadi.

Kasar Iran ta yi kira da a dakatar da matakan sojin da kasar Saudiyya ke jagoranta kan kasar Yemen. An jiyo ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif na cewa kasarsa za ta yi duk abin da ya dace na shawo kan rikicin na kasar ta Yemen. A kuma wata hira da ya yi da Firaministan Birtaniya David Cameron ta wayar tarho, shugaban Iran Hassan Rouhani ya soki matakin sojin da ake dauka kan Yemen din. Jiragen saman yakin Saudiyya da kawayenta na kasashen Larabawa sun kai hare-hare kan dakarun Huthi da ke kokarin kifar da shugaban Yemen Abd-Rabbu Mansour Hadi mai samun daurin gindin kasashen yamma. A kuma halin da ake ciki shugaba Mansour Hadi ya sauka birnin Riyadh na Saudiyya.