1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran na ci gaba da bijerawa Trump

April 6, 2026

Iran ta gargadi shugaban Amurka Donald Trump kan kuskuren aiwatar da barazanar kai wa ababen more rayuwa da gidajen fararen hula na kasar hari saboda takaddamar bude mashigar Hormuz.

https://p.dw.com/p/5BjMn
Iran Teheran 2026 | Plakat zur Schließung der Straße von Hormus
Hoto: AFP

Iran ta kaddamar da sabbin hare-hare a Litinin din nan kan Isra'ila da wasu kasashen yankin Gulf ciki har da Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa, tare da yin gargadin kai samame masu muni a matsayin ramuwar gayya muddin shugaban Amurka Donald Trump ta aiwaztar da barazanar da ya yi wa kasar.

Trump ya tsawaita wa'adin da ya bai wa Iran da sa'o'i 24

Daga nata bangare Isra'ila ta sanar da yin barin wuta kan birnin Teheran, inda talabijin na gwamnati ya ruwaito cewa an kai hari da ya lalata wani wurin sarrafa iskar gas da ke kusa da wata jami'a, lamarin da ya janyo katsewar gas a wasu sassan birnin. Hakazalika wasu kafafen yada labaran Iran sun ruwaito cewa an kai wasu hare-hare a unguwannin zaman jama'a na birni Tehran.

A cikin wata sanarwa cewa kakakin rundunar sojin Iran ya yi gargadin cewa : idan hare-haren kan fararen hula suka ci gaba, mataki na gaba da Iran za ta dauka ya kasance mafi muni, yayin da Trump ya bukaci Iran ta bude mashigar Hormuz kafin zuwa karfe takwas da daren gobe Talata ko kuma ta dandana azaba.

A ranar yau ne ake sa ran shugaba Trump zai yi taron manema labarai a fadar White House domin yin bayani kan ceto matukin jirgin yakin Amurka da Iran ta harbo a ranar Juma'a.