1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ina makomar jam'iyyar ADC?

April 28, 2026

A yayin da ake kara kusantar zabuka a Tarayyar Najeriya, daga dukkan alamu jam'iyyar ADC ta adawa na neman komawa dashi mai rai guda tara.

https://p.dw.com/p/5Cy4M
Najeriya | Abuja | Taro | ADC | 2026
Babban taron jam'iyyar adawa ta ADC a NajeriyaHoto: Uwaisu Abubakar Idris/DW

Wata sabuwar kara dai yanzu haka, na neman soke rijistar jam'iyyar kan hujjar kasa cimma ka'idojin ci gaba da zama jam'iyya ta siyasa a Tarayyar Najeriya. Wata kungiyar da ta kira kanta ta tsofaffin 'yan majalisun tarayyar Najeriyar dai, ta ce ba hujjar kyale ADC da wasu jam'iyyu hudu su taka rawa cikin fage na siyasar kasar a halin yanzu. Tsofaffin 'yan dokar dai sun nemi wata kotu da ke zama a Abuja da ta soke rijistar ADC da wasu jam'iyyu hudu, bisa zargin kasa cimma tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar tare da neman kotu ta tilasta Hukumar Zabe mai Zamna Kanta ta Kasar INEC cire sunan ADC cikin sahun jam'iyyun da ke shirin taka rawa a zabuka masu zuwa.

Ko INEC za ta soke jam'iyyar ADC?

Akwai yiwuwar mai shari'a Peter Lifu da ke jagorantar kotun, zai saurari sabuwar karar da ta kara fito da tarnakin da ke gaban ADC fili. ADC dai ta fito cikin babban zabe na shekara ta 2023 da dan majalisar wakilai daya tilo, ba kuma tare da samun nasarar kaso 25 cikin 100 ko da a jiha daya ba duk da kai wa ga fidda dan takara a zaben. To sai dai kuma har ya zuwa kidan kuge na zabuka na shekarar badi dai, babu matakin soke ta a bangaren INEC da ke da karfin ikon soke jam'iyyu na kasar.

Dalilan Tambuwal na sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC

Laifi can baya hukunci a gaba ko kuma kokarin haddasa rikici, daga kotun koli zuwa kotunan da ke kasa ADC na fuskantar shari'u iri-iri a kan hanyar kai wa ga takara a zaben na badi. Akwai dai tsoron ci gaba cikin kwarafniyar banar na iya tsinke igiyar gugan da ke ta kokarin kara matsawa zuwa ruwan na siyasa, amma kuma a cikin rikicin da ke da girman gaske. Sanata Ahmed Babba Kaita dai na zaman jigo a jam'iyyar ADC ta adawa, kuma ya ce ba sa tsoron shari'a cikin batun na siyasa. Kada cikin ruwa na siyasa ko kuma kokarin murde adawa, ya zuwa yanzun dai duk da kokarin yin ta maza daga dukkan alamu shari'un na tasiri a cikin harkokin jam'iyyar.

Yaushe ADC za ta yi zaben fidda gwani?

Akalla mako guda da bude wa'adin takarar fidda gwanaye dai, har ya zuwa yanzu 'yan ADC sun gaza sanya lokaci na sayar da takardar izinin takara a zaben na badi balle  gudanar da zabukan fitar da gwanayen. Farfesa Kamilu Sani Fagge na sharhi cikin siyasa ta kasar, kuma ya ce sabon salon na barazana ga makomar dimukuradiyyar Najeriyar. Najeriyar dai tana kara shiga rudanin na siyasa, cikin rashin tsaro da karuwar talauci a tsakanin miliyoyin 'yan kasar.

 

Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani