Ikirarin kafa Daular Musulunci a Najeriya | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 29.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ikirarin kafa Daular Musulunci a Najeriya

Kungiyar Boko Haram da ke fafatawa da dakarun Najeriya a yankin arewa maso gabashin kasar, ta yi koyi da 'yan ta'adda na kungiyar Islamic State a Iraki da Siriya.

Bari mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda a wannan makon ta mayar da hankali kan tarayyar Najeriya tana mai cewa shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya ayyana kafa daular Musulunci bayan ta kwace wani gari a arewa maso gabashin Najeriya.

Bisa ga dukkan alamu kungiyar 'yan ta'adda a Najeriya tana son ta yi koyi ne da kungiyar 'yan ta'dda ta Islamic State a Iraki da Siriya. Sai dai a cewar jaridar kungiyar ta Boko Haram tana rashin muhimman tanade-tanade da tsare-tsare idan aka kwatantata da kungiyar IS. To amma wannan ikirarin kadai ya nuna a fili irin raunin gwamnatin Najeriya. Tun a farkon watan Agusta ne Boko Haram ta yi wa yankin dirar mikiyya ta kone gidajen mutane sannan ta kwace fadar basaraken garin. Abin da ke a fili shi ne yanzu rikicin ya zama wata farfaganda tsakanin Boko Haram da gwamnati. Domin jim kadan bayan sanar da kafa daular Musuluncin, sojojin Najeriya sun karyata wannan ikirari na Shekau suna masu cewa dukkan yankunan Najeriya suna nan karkashin ikon gwamnati, kuma dakarun kasar suna fafatawa da masu tayar da kayar baya a yankunan da lamarin ya shafa."

Fargabar zuwa Afirka saboda Ebola

Har yanzu dai annobar cutar Ebola da ta addabi yankin yammacin Afirka na ci gaba da daukar hankalin jaridun na Jamus. A labarin da ta buga jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce fargaba sakamakon cutar Ebola a Afirka.

"A dangane da cutar ta Ebola, wasu kamfanoninn zirga-zirgar jiragen sama na Turai suna yi wa yankunan da ke fama da annobar cutar dan wake zagaye. Duk da kokarin da hukumar lafiya ta duniya ke yi ba dare ba rana na kwantarwa da hankali tare da yin bayanin cewa babu wani dalilin soke zirga-zirgar jiragen saman a wannan lokaci. Ita ma Majalisar Dinkin Duniya gargadi ta yi cewa soke zirga-zirgar jiragen saman zai sa matsalar kwayoyin Ebola ta kara yin muni, domin zai hana likitoci masu kokarin kai taimakon da ake matukar bukata. To amma duk da wannan gargadin Air France da British Airways sun dakatar da zirga-zirgar jiragensu zuwa yamacin Afirka sannan yanzu haka wasu kananan kamfanonin jiragen sama sun bi sahunsu. Tun yanzu wannan matakin ya fara janyo mummunan tasiri ga kokarin magance yaduwar kwayoyin cutar."

Rige-rigen sayen filayen noma a Afirka

Tserereniyar mallakar gonaki a kasashe masu tasowa, inji mujallar Der Spiegel, sannan ta ci gaba kamar haka.

"Habakar cinikin makamashin da ake sarrfawa daga tsirrai ita ce babban dalilin da ya yanzu masu zuba jari na kasa da kasa suke rige-rigen sayen manyan gonaki a kasashe masu tasowa. Yanzu haka wadannan kamfanoni suna da hannun wajen sayen kashi daya bisa hudu na gonakin tsirrai irinsu soya, rake ko kwakwan man ja, da ake sarrafa makamashin da su. Mujallar ta ce musamman masu zuba jarin na kasa da kasa sun fi mayar da hankali a kasashen Afirka na Kudu da Sahara. Kamfanonin Birtaniyya sun fi yawa a jerin masu sayen filin don noman tsirrai saboda makamashi, matakin da masu suka suka ce yana janyo nakasu wajen noman kayan abinci don rage matsalar karancin cimaka a kasashen Afirka.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman