1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Human Rights Watch ta gargadi Najeriya

September 17, 2018

Kungiyar Human Rights Watch ta bukaci gwamnatin Najeriya ta hukunta wadanda da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram bisa amincin tsari na duniya.

https://p.dw.com/p/350bu
Nigeria Boko Haram
Hoto: DW/Al-Amin Suleiman Mohammad

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta bukaci gwamnatin Najeriya ta tabbatar da hukunta wadanda da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne da ke tsare, bisa tsari da duniya ta amince da shi.

Human Rights Watch ta yi wannan kiran ne dai dai lokacin da ake nuna damuwa kan yadda ake tafi da aikin hukunta mayakan na Boko Haram, musamman ma tsawon lokaci da batun ke dauka.

Cikin watan Oktobar bara ne aka fara shari'ar wadanda da ake zargin zama 'yan kungiyar su 1,669, a jihar Neja da ke arewacin Najeriyar, abin da aka yi marhabin da shi daga bangarori da dama.

Kungiyar ta Human Rights Watch na cewa ne muddin aka saba tsari a shari'ar, to hakan ka iya tabarbara rikicin na Boko Haram da Najeriyar ke a ciki.