Hulda za ta gyartu tsakanin EU da Turkiyya
September 9, 2016Talla
Babbar Jami'ar harkokin waje ta kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini da kwamishina mai kula da fadada wakilci a kungiyar tarayyar Turai Johannes Hahn wadanda ke wata muhimmiyar ziyara ta kololuwa a Turkiyyar sun ce za'a bude sabon babi kan shirin karbar kasar a Kungiyar ta EU yayin da batun sassaucin Visa kuma za'a ci gaba da tattaunashi. A baya-bayan nan manyan jami'ai na Turkiyya da kungiyar tarayyar Turai sun yi ta cacakar baka bayan yunkurin juyin mulkin inda Hedikwatar tarayyar Turai a Brussels ta yi kakkausar suka kan tsauraran matakan da Turkiyya ta dauka yayin da fadar gwamnatin a Ankara kuma ta soki tarayyar turai da rashin nuna goyon baya.