1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kisa na matukar karuwa a duniya

Suleiman Babayo MAB
May 16, 2023

A shekarar 2022, kimanin mutane 883 aka zartas ma hukuncin kisa a cewar kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya Amnesty International. Adadin ya fi yawa a kasashen Iran da Saudiyya, baya ga fursunonin siyasa

https://p.dw.com/p/4RRdX
Iran na cikin jerin kasashen da suka fi aiwatar da hukuncin kisaHoto: picture alliance/Wolfram Steinberg

Misalin daya daga cikin wadanda suka fuksanci hukuncin shi ne Mohammed Mehdi Karimi dan wasan karate na kasar Iran mai shekaru 22 da haihuwa. Dan majalisar dokokin Jamus na Bundestag, Helge Limburg yana tune da wannan rana ta 7 ga watan Janairu da aka aiwatar da hukuncin, saboda dan majalisar na jam'iyyar kare muhalli na cikin masu daukan nauyin irin wannan matasa da suke wasa, duk da yake ba su taba haduwa ba, amma hukuncin kisan matashin ya jijjiga shi.

Iran | Öffentliche Erhängung von vier Männern in Isfahan
Hukuncinn kisa na shan tofin Allah tsine a sassan duniyaHoto: Baharlo Jam/abaca/picture alliance

 Helge Limburg ya kara da cewa: "Amincewa da hadakar a farko an yi bisa tafarkin siyasa ne da nuna goyon baya ga 'yan adawa na Iran. Amma daga bisani aka kulla abokantaka duk da yake ban taba ganin Mehdi ba ko waya da shi ba. Na yi kokarin binciken samun na kusa da shi lokacin da na ji. Na yi matukar bakin ciki kan samun labarin kisan. Wannan rana ce da ke cike da bakin ciki ga ni da kuma iyalaina da suka ji abin da ya faru."

Iran da Saudiyya na sahun gaba wajen aiwatar da hukuncin kisa

A shekarar da ta gabata, kimanin mutane 576 ne kasar Iran ta zartas musu da hukuncin kisa adadin da ya yi kusan ninka na shekara ta 2021. Yayin da shekara ta 2021, kasar Saudiyya ta yanke hukuncin kisa kan kimanin mutane 196. Alkaluman mutane 883 da suka fuskanci hukuncin kisa a shekarar da ta gabata ta 2022, an tattara ne a kimanin kasashen 20.Babu kasar Chaina a ciki, duk da ana zaton ta aiwatar da hukuncin kan dubban mutane ko kuma kasar Koriya ta Arewa da babu wanda yake da masaniyar irin abin da ke faruwa na mutanen da suke fuskantar hukuncin kisa.

Hannover Messe 2023 | Begleitveranstaltung zur Eröffnung
Amnesty International ta saba yin tir da hukuncin kisaHoto: Arti Ekawati/DW

Boris Mijatovic mai magana kan kwamitin kare hakkin dan Adam na majalisra dokokin Jamus ya ce tilas a ci gaba da muhawara kan batun. Ya ce " Idan na tuna sau da yawa na kan yi jayayya wajen cewa babu wanda yake da ikon daukan rai. Domin haka babu wani mutum da ya dace a rataye shi. Haka ake fama da kasashen yankin Gulf da Asiya ko kuma arewacin Amirka, inda sai mutum ya yi dogon tunani kafin samun ci-gaba saboda tsawon lokaci da aka kwashe kan batun. Mun haramta hukuncin kisa a Turai. Mun yi muhawara sosai da suka hada da Faransa, idan zan iya tunawa. Na yi farin ciki da inda muka kai."

A nahiyar Afirka, ana samun ci-gaba inda kasashe ke ci gaba da soke hukuncin kisa.