1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta saurari 'yan jam'iyyar PDP

May 22, 2017

Kotun kolin Najeriya ta yanke hukunci a cikin zagaye na farko na takaddamar da ke a tsakanin bangarori guda biyun babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

https://p.dw.com/p/2dOvE
Karikatur Nigeria PDP Krise
Hoto: DW

An dai wayi gari a cikin fata bisa samun haske a cikin rikicin jam’iyyar PDP ta adawa a tsakanin Ali Sheriff da ke zaman tsohon gwamna a Jihar Borno da kuma Ahmed makarfi da ya mulki Kaduna amma kuma duk ke gwagwarmaya ta ruhin PDP yanzu. To sai dai kuma an kai yamma tare da wni hukuncin da ya kara karfin gwiwa ga Makarfin da tunda farkon fari bangaren na Sheriff ya nemi kotun da ta hana Makarfin shigar da kara.


Lauyoyin na Sheriff dai sun ce ya zamo na wajibi ga Makarfin nemi izizni a bangare na Sheriff din kamun iya kai wa ga samun kunnen kotun da ke zaman zangon karshe da kuma ke iya yin tasiri ga makomar jam’iyyar. Bayan dogon Turanci da mahawarar da ta dauki lokaci, alkalan kotun a bisa 'yancin na Makarfi na samun damar yin karar dama iya samun nasara in ta kama.

Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler


Abun kuma da bangaren na Makarfi suka fassara a matsayin babbar nasara da alamu na irin abin da suke shirin gani nan gaba a cikin kotun. Abun jira a gani dai na zaman iya shawon kan banbancin tare da fuskantar zaben da ke tafe da zuciya guda ga PDP da a baya ta sha alwashin har mahdi, amma kuma mahdin ke neman wucewa da saninta a yanzu.