1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama maharin shagunan Turkawa

Ramatu Garba Baba
July 23, 2021

Wata kotu da ke birnin Munich ta zartas da hukuncin sama da shekaru 9 kan matashin da yayi kaurin suna a kai hare-hare kan wuraren kasuwancin Turkawa mazauna Jamus.

https://p.dw.com/p/3xwCO
NSU-Prozess zweiter Auftakt
Hoto: REUTERS/Kai Pfaffenbach

A wannan Juma'a, kotun ta zarta da hukuncin zaman gidan yari na shekaru tara da rabi kan mutumin da aka samu da laifin kassara kasuwancin wasu Turkawa mazauna Jamus. An kiyasta asara na euro miliyan hudu a sakamakon jerin hare-harensa.

Asali ma dai, kotu ta same shi da laifuka har ashirin da shida, ciki har da yunkurin kisan kai a sanadiyar wutan da ya taba cinna wa kan wani shagon wani dan asalin kasar Turkiyya da ke a jahar Baveriya da shirinsa kitsa kai hari kan ofishin jakadanci da wani masallaci na Turkawa da ke biranen Munich da Kolon, ya kuma ce yana shirin kai ma limamai hari, sai dai daga karshe ya ce, yayi nadama.

An gano yadda ya kwashi tsawon lokaci yana koyon yada ake hada abubuwan fashewa daga shafin intanet na mayakan Kungiyar IS, da ya ke amfani da su, kafin a watan Mayun bara, jami'an tsaro su yi nasarar cafke shi. Ba a yarda an bayyana sunan maharin da kuma asalinsa ba.