Hukumomin Nijar sun tabbatar da mutuwar mutane16 | Labarai | DW | 18.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumomin Nijar sun tabbatar da mutuwar mutane16

Mayaƙan Ƙungiyar Boko Harm sun kashe mutanen ne a harin da suka kai a wani ƙauyen da ke cikin BosSo a gabashin Diffa

Hukumomin tsaro a Nijar sun tabbatar da cewar aƙalla mutane guda 16 suka mutu a harin da Boko Haram ta kai a wani ƙauyen da ke cikin Boso da ke a gabashin ƙasar cikin jihar Diffa.

Gidan telbijan mallakar gwamnati na Nijar ɗin ya ambato magajin garin Bosso Bako Mamadou,yana mai cewar mayaƙan sun buɗe wuta a lokacin harin na ranar Larba a kan wasu jama'ar a lokacin da suke cikin yin sallah. Nan take mutane 15 suka cikka kana ɗaya ya mutu sakamakon raunikan da ya samu daga bisani yayin da wasu huɗu suka jikkata.