Hukumar ′yan gudun hijira ta duniya za ta samu karin Euro miliyan 61 | Labarai | DW | 07.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar 'yan gudun hijira ta duniya za ta samu karin Euro miliyan 61

Jamus za ta ba wa hukumar Euro miliyan 61 don tafiyar da aiki a yankuna masu fama da rikici na Afirka.

Tarayyar Jamus ta yi alkawarin ba wa hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNHCR karin Euro miliyan 61 a bana don gunadar da aikinta a yankuna masu fama da matukar rikici na Afirka. Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ba da wannan tabbacin a wannan Litinin bayan wani taro da ya yi da kwamishinan kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya Filippo Grandi a birnin Berlin. Ministan ya ce ko da yake matsalolin 'yan gudun hijira a Siriya da makwabtanta za su ci gaba da daukar hankalin Jamus, amma kasar ta damu ainun da wahalhalun da ake fama da su sakamakon rikice-rikice a yankin tafkin Chadi da Sudan ta Kudu da Somaliya da kuma Burundi. Ministan ya kara da cewa yanzu haka kasashen Afirka Kudu da Sahara su ne suka karbi bakoncin mafi yawan 'yan gudun hijira a duniya baki daya. Karin kudaden dai za a kashe su ne a aikin jin kai musamman ga 'yan gudun hijira a Burundi da Mali da Somaliya da Sudan ta Kudu da kuma wadanda rikicin Boko Haram ya tilasta musu barin yankunansu na asali musamman a yankin tafkin Chadi.