Hukumar Lafiya ta ce cutar Ebola za ta shafi mutane 20,000 | Labarai | DW | 29.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar Lafiya ta ce cutar Ebola za ta shafi mutane 20,000

Annobar cutar Ebola tana ci gaba da ta'adi cikin kasashen Afirka ta yamma inda fiye da mutane 1,500 suka hallaka

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce barkewar cutar Ebola da aka samu a wasu kasashen yankin yammacin Afirka za ta shafi fiye da mutane 20,000. Sannan ta yi gargadin cewa yunkurin kasashen duniya na dakile cutar zai lakume kimanin dalar Amirka milyan 500.

Hukumar ta ce ana yunkurin samar da rigakafin cutar ta Ebola wanda za a yi kwaji kan mutane. A wannan Alhamis da ta gabata mahukuntan Najeriya sun bayyana mutuwar wani likiti a birnin Fatakwal fadar gwamnatin Jihar Rivers, wanda ya yi jinya daya daga cikin mutanen da suka yi ma'ammala da dan Laberiya da ya kai cutar kasar.

Hukumar Lafiyar ta kuma yi gargadi kan illar rufe iyakoki bisa tsoron yaduwar cutar ta Ebola, yayin da ministocin lafiya na kasashen Afirka ta yamma ke taro a birnin Accra na kasar Ghana.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman