Hukumar CNDH za ta sasanta rikicin Nijar | Siyasa | DW | 23.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hukumar CNDH za ta sasanta rikicin Nijar

Bayan da hukumomin kasa da kasa ciki har da OIF sub gaza shawo kan rikicin siyasar Nijar, hukumar kare hakin dan Adam CNDH ta sha alwashin dinke barakar tsakanin bangarorin Ilmi da siyasar kasar.

Hukumar ta bayyana matakin shiga tsakanin bangarorin siyasa da basa ga maciji da juna, da ma bangarorin malaman makarantun jami'a da daliban su da kuma malamai da gwamnati a wani mataki na yayyafa ruwan sanyi ga zukatan 'yan siyasar kasar a gabanin zabukan da ke tafe masu cike da kalubale, Mal. Assoumana Moussa Kwamishinan kare hakkin dan adam ne da ke hukumar ta CNDH.

Niger Niamey Opposition (DW/M. Kanta)

Wasu jagoririn jam'iyar Adawa a Nijar

"Muna kokarin ganin yanda za mu tattara su a wuri guda, idan har mun sadu da su tare da sauraren kowa to sai mu gani muna iya hada su ko kuwa a a: Burin mu shi ne gyara wannan kasar, saboda tamu ce kasar mu duka. Idan ta gyaru dadin kowa ne, idan kuma ta lalace zai yi wa kowa zafi."

Wasu daga cikin 'yan siyasa sun bayyana wannan yunkuri a mastayin jigo da zai dinke barakar siyasa, kamar yadda Mal. Annabo Soumaila Shugaban Jam'iyyar PNDN ke cewa.

Mamadou Karidjo (DW/M. Kanta)

'Yan siyasa a Nijar

"Muuna son sulhu domin da ba haka ba, da duk mutanen da suke aiko muna a waje da ba mu saurarensu ba."

Suma dai a na su bangaren gungun kawancen jam'iyyun da ke mulki cewa suka yi, ba tun yau ba suke fatar ganin 'yan adawar sun sake dawowa a matsayinsu, domin ganin an yayyafawa danbarwar siyasar ruwar sanyi. Acewar su kullum suna jan hankalin shugaban kasa da ya kira a zauna tare amma sun kiya. To idan mutun ya ki ya za ka yi da shi? Sau nawa a ke kiransu idan har basu zo ba zaben fa yin shi za a yi  da su ko ba da su.