Hollande zai kai ziyara Afirka | Labarai | DW | 06.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hollande zai kai ziyara Afirka

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande zai kai wata ziyarar aiki zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ke fama da rikicin addini.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande

Wannan rikici dai ya kusa rikidewa izuwa yakin basasa. Rahotanni sun nunar da cewa Hollande zai kai ziyarar ne a ranar 13 ga wannan wata na Mayu da muke ciki, a wani yunkuri na yin alkawarin da ma nuna samun goyon bayan Faransa a shirin zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar domin kawo karshen rikicin da kasar ta yi fama da shi. Kana ana sa ran Hollande zai zarce Tarayyar Najeriya a ranar 14 ga watan na Mayu domin halartar taron yankin Afirka ta Yamma da zai mayar da hankali kan yaki da kungiyar ta'addan Boko Haram da ta addabi Najeriya da wasu makwabtanta.