Himma dai Matasa: Mai sayar da kaya ta internet | Himma dai Matasa | DW | 03.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Himma dai Matasa: Mai sayar da kaya ta internet

Matashin da ya rungumi sana'ar saye da sayar da kayan sawa na Afirka ta kafafen sada zumunta na zamani, domin dogaro da kansa.

Bildergalerie Afrikanische Modedesigner in Portugal

Saye da sayar da kayan sawa na Afirka ta kafafen sada zumunta na zamani

Matashi mai suna Abdoulrazak Hima Sido da ke da shekaru 27 a duniya, ya kama wannan sana'ar ne bayan da kammala karatunsa na digiri, inda ya karanci fannin aikin hukuma. Ya kuma bayyana cewa, tun yana yaro sana'o'i ke birge shi kasancewar ya tasao gidansu ana yin sana'o'i. Ya kara da cewa ya fara sana'ar ne bayan da ya ga wata mata ta saka kayayyakin a shafinta na Facebook tana tallansu.

Abdoulrazak ya bayyana cewa daga lokacin da ya dauki lambar matar suka yi magana ne sai ta fara turo maa da kayan inda shi ma yake dorawa a kafafensa na sada zumunta. Ya kara da cewa kwalliya ta biya kudin sabulu da wannan sana'a tasa. Sai dai Abdoulrazak ya nunar da cewa, duk da nasarorun da ya samu akwai kalubale, inda babbar matsalar ita ce ta rashin karfin internet da kuma yadda wasu kan ce suna son kaya ya ajiye musu, daga bisani kuma suce sun fasa. 

Sauti da bidiyo akan labarin