Helmut Kohl ya mutu yana da shekaru 87 | Duka rahotanni | DW | 16.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duka rahotanni

Helmut Kohl ya mutu yana da shekaru 87

Tsohon shugaban gwamnatin Jamus, mutum ne wanda zai dade a zukatan al'umma saboda irin rawar da ya taka a siyasa, musamman bisa gudunmawar da ya bayar na hadewar Jamus da ma siyasar nahiyar Turai

 

Da aka tambaye shi yadda zai ji idan aka yi mutun mutumin shi, a matsayin karrama shi, ya amsa cikin raha ya ce da zarar baki suka tafi, tantabaru ne zasu fara zuwa, sannan sai karnuka da sauransu.  Ana iya cewa bayan faduwar bangon Berlin Helmut Kohl ya kasance mafi suna a tarihi, ya ma zama tamkar mutun-mutumin da ke raye, wannan kadai ya dora shi bisa sauran sao'insa masu rike da iko. Wadanda ke sukan shi a cikin jam'iyyarsa sun yi ta kokarin kawar da shi, su yi mi shi juyin mulki, da kyar da sudin goshi ya samu ya rike karfin shi a jam'iyyarsa ta CDU. 

Da yawa na mi shi kallon mai kwarewar gaske a fanin siyasa domin yana da dabaru na hangen nesa, kuma ya san yadda zai hada wannan da matakai masu nagarta. A dalilin wannan kwarewar ne ma ya kafa tarihi domin da bangon Berlin ya fadi, sai ya yi amfani da shi a matsayin dama ta hada kan 'yan kasar baki daya. Ana iya tuna wannan da jawabin da ya yi a wancan lokacin a birnin Dresden

"Haka kuma ku bar ni in yi wani karin bayani a wannan dandalin na mu na gargajiya. Buri na zai cika idan muka kafa tarihi na hadin kan kasarmu"

Makwanni uku kacal bayan faduwar bangon ya gabatar da taswirar hanyar da za ta tabbatar da hadin kan Jamus ga Majalisar dokokin Bundestag, mai shawarwari goma. Bai tsaya nan ba, ya kuma nemi hanyar kawar da jita-jita a kasashen waje, ya kawar da shakkun duk masu tababar yiwuwar wannan shiri na sa. 

Ko lokacin mulkinsa ma an ga abubuwa masu kayatarwa, kamar kawancen da ya kulla da Faransa, sulhun da aka yi da kasar Poland  da yadda ya rika kullawa da kasashen da ke tasowa, na tsohouwar daular sobiet, duk alamu na wanda siyasarsa ke yunkurin tafiya da kasashe makota.

Guido Westerwelle, Ex-Außenminister FDP - 80. Geburtstag Helmut Kohl (picture-alliance/Augenklick/B. Kunz)

Ministoci da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sunkuye a gaban Helmut Kohl

A tarihin rayuwarsa, yakin duniya na biyu na taka rawar sosai, domin yayansa ya kasance soja a wancan lokacin kuma ya mutu a yakin, abin da ya tsaya da shi duk tsawon rayuwarsa. Ko yadda aka raba Jamus zuwa yankin gabashi da yammaci ya shafe shi domin a lokacin da ma aka kammala yakin, shekarunsa na haihuwa15 ne kadai. A wannan shekarun dai ba zai iya daukar nauyin Jamus ba, amma kuma a shekarar 1989 ya yi wani jawabi mai sosa rai a majalisar dokokin Bundestag

"Na yi tayin cewa zan fadada tallafi da aiyukan da muke yi tare, idan muka sauya tubalin da muka girka dangane da tattalin arziki da siyasa, ya zo dai dai da na yankin gabashin Jamus wato DDR kuma a mayar da su dokoki irin wadanda ba za'a iya sauyawa ba."

Kohl ya kasance yaro a lokacin yaki kuma ya zama matashi cikin barabuzan da yakin ya bari, a dalilin haka ne ya kasance daga cikin zuri'ar da suka sha alwashin cewa ba zasu yarda a sake ganin irin wannan lamari ba. Daga nan kuma ya kuduri aniyar shigar da Jamus cikin Turai, bayan shekarar 1990 lokacin da ta kara girma

Ya kuma iya kafa tarihi a wurare masu mahimmanci kamar lokacin da ya rike hannun, dan jam'iyyar Socialist na Faransa Francois Mitterand a makabartan da aka rufe sojojin da suka fadi lokacin yakin duniya na farko. Kohl ya mayar da batun hadin kan Turai alhakin Jamus. Da karfin shi ya yi gwagwarmayar ganin an samar da takardar kudin euro abin da ta kasance wata alama ta siyasa a wurin shi, ya kuma kusan tilasta hadin kai da yankin gabashin Turai kuma daga karshe aka kafa kungiyar Tarayyar Turai. 

Ya ce: "Takardar kudin euro na bai daya, abu ne da zai tabbatar da daidaito da hadin kan Turai , kuma wannan na tabbata, a tare zamu karfafa zumunta tsakanin kasashen Turai. Kuma takardar kudin euro zai tabbatar da haka, zai baiwa al'ummar Turai daman zama tare su gina makomar da suke bukata"

Za a cigaba da tunawa da shi a matsayin dan adam, wanda ya banbanta daga Willy Brandt shi ma mai hangen nesa ko kuma Helmut Schmidt wanda ya nakalci tattalin arziki. Shi ya kasance dan siyasa mai kiima a idon jama'a