Hayakin man Diesel na haddasa cututuka | Labarai | DW | 08.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hayakin man Diesel na haddasa cututuka

Wata kididiga da wata cibiya ta kwararru ta fitar a Jamus ta nuna cewar hayakin da motocin da ke yin amfanin da man Disel suka saki a shekara ta 2014 ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu shida a sakamakon cututuka.

Tururin hayakin wanda kan turnike cikin sararin samaniya na haddasa cututukan da suka shafi bugon zuciya kamar su hawan jini da cutar suga da cututukan da suka shafi huhu irinsu asthma. Kididgar ta ce kishi takwas na wadanda ke fama da ciwon suga a Jamus da kuma kishi 14 na masu fama da asthma tururin hayakin ne dalilinsa.