1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hatsin Rasha ga kasashen shida na Afirka

Suleiman Babayo AH
February 21, 2024

Rasha ta kammala shirin ba da kyautar hatsi ga wasu kasashe shida na Afirka kyauta bisa taimakon da ta yi alkawari tun shekarar da ta gabata.

https://p.dw.com/p/4chID
Rasha | Hatsi daga yankin Rostov
Hatsin RashaHoto: Sergey Pivovarov/SNA/IMAGO

Ma'aikatar aikin gona ta Rasha ta bayyana kammala shirin tura kimanin hatsi ton-dubu-200 zuwa kasashen Afirka guda shida kyauta, kamar yadda Shugaba Vladimir Putin na kasar ta Rasha ya yi alkawarin ga shugabannin kasashen a shekarar da ta gabata.

Ministan ma'aikatar noma Dmitry Patrushev na kasar ta Rasha ya tabbatar da haka a wani sakon da aka wallafa a wannan Talata da ta gabata, inda kasashen Somaliya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kowacce za ta samu ton dubu-50, kana sauran kasashen Mali da Burkina Faso, da Zimbabuwe da Eritrea kowacce ton dubu-25.

Matakin yana cikin shirin Rasha na rage radidnin yaki da ke faruwa tsakanin kasar da Ukraine, abin da ya haifar da tsadar hatsi, kuma lokacin ganawa da shugabannin na Afirka ne gwamnatin ta Rasha ta yi alkawarin ba da taimakon ga kasashen kyauta.