'Yan sanda na bincike kan harin wuka a Jamus
July 21, 2018Talla
Mai shekaru 34 a duniya, an zarge shi da kokarin yin kisa da yin munanan raunuka ga mutane da kuma haddasa gobara da gangan da nufin raunata mutane. Maharin wanda har kawo yanzu bai ce komai kan dalilinsa na kai wannan harin ba, ya kunna wuta a jakarsa ta goyo a cikin motar kirar Bus da ke dauke da fasinjoji, kana ya yanki mutane 10 da wuka. Fasinjojin da ke cikin motar ne dai suka hada karfi wajen damke shi tare da mika shi ga jami'an 'yan sanda.