Harin Boko Haram ga sojojin kasar Chadi | Labarai | DW | 06.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin Boko Haram ga sojojin kasar Chadi

Da asubahin wannan Talatar ce mayakan kungiyar Boko Haram suka kai wani mumunan hari ga dakarun sojan kasar Chadi da ke bakin iyakar kasar da Najeriya.

Rahotanni daga birnin Djamena na kasar Chadi na cewa, mayakan Boko Haram sun hallaka sojojin kasar a kalla 11 a wani hari da suka kai musu da asubahin wannan Talatar a garin Kaiga Ngouboua da ke da nisan km biyu da iyakar kasar da Nageriya kusa da Tafkin Chadi. Wata majiya ta jami'an tsaron kasar ta Chadi, ta tabbatar wa kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP mutuwar sojojin 11, cikinsu har da wani Laftanan kanal na sojan kasar ta Chadi, yayin da wasu 13 suka jikkata.

Daga nasu bangare sojojin na Chadi sun kashe 'yan Boko Haram a kalla 17 sannan suka ci gaba da biyarsu bayan da suka koresu. Tun dai farkon wannan shekara ce dakarun kasar ta Chadi ke yakar 'yan kungiyar ta Boko Haram, wadda ta fadada ayyukanta na kai hare-hare a kasashen na Chadi, Kamarun da kuma Nijar.