Harin bam ya hallaka mutane da dama a Turkiya | Labarai | DW | 21.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya hallaka mutane da dama a Turkiya

Akalla mutane 50 ne suka mutu yayin da wasu kimanin 100 suka samu raunuka a wani harin bam da aka kai lokacin da jama'a ke tsakiyar shagulgullan aure a birnin Gaziantep

Türkei Explosion bei Hochzeit in Gaziantep

Inda aka kai harin bam a birnin Gaziantep

Cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta Turkiya ta fitar a wannan Lahadin, Shugaba Recep Tayyip Erdogan, ya ce suna tsammani kungiyar IS ce ke da alhakin kai wannan hari. Inda sanarwar ta kara da cewa babu wani bambanci tsakanin malamin nan dan kasar ta Turkiya Fethullah Gülen da ake zargi da shirya juyin mulkin da bai yi nasara ba, da jam'iyyar Kurdawa ta PKK, da kuma kungiyar IS da suke zargin ita ce ta kai wannan hari na birnin Gaziantep da ke Kudu maso Gabashin kasar ta Turkiya, wanda ke a nisan kilo mita 60 da iyakar kasar Siriya. Shugaba Erdogan ya kara da cewa, harin da Kurdawan PKK suka kai a watan da ya gabata ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 70.