PKK kungiya ce ta Kurdawa da ke kasar Turkiyya. Hukumomin kasar na daukar kungiyar a matsayin ta 'yan ta'adda.
A cikin shekarar 1978 ne aka kafa kungyiar ta PKK kuma wasu dalibai ne a Turkiyya din suka girka wannan kungiya. Kurdawa su ne kashi 20 cikin 100 na al'ummar Turkiyya.