Hari ya hallaka mutane hudu a Najeriya | Labarai | DW | 16.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya hallaka mutane hudu a Najeriya

An samu alkaluman wadanda suka mutu a harin Bam na Maiduguri fadar gwamnatin Jihar Borno da ke Najeriya.

Akalla mutane uku ciki har da wani farfesa ne suka mutu, yayin da wasu 15 suka jikkata, a wani harin bom da aka kaddamar kan masallata a wani masallacin da ke a rukunin gidajen ma'aikta na jami'ar Maiduguri a Najeriya.

Bayanan baya-bayan nan sun ce, harin wanda aka kaddamar lokacin sallar asubahin yau Litinin, ya faru ne yayin da wata 'yar yarinya ta tada bom din da ta kunsa a jikinta.

'Yan sanda sun ce kafin ma tashin bom din na masallacin jami'ar, sun harbe wata 'yar yarinyar da suka kiyasta shekarunta kimanin goma sha biyu, da suka ce tana yunkurin shiga jami'ar, a lokacin da suke sintiri da karfe biyar da kwata na asubahi.

Wannan dai shi ne karo na farko da ake kaddamar da hari a jami'ar ta Maiduguri tun shekarun da wutar rigimar tsaro ta kunnu a yankin.

Zuwa yanzu dai ba a kai ga samun wadanda suka dauki alhakin harin na yau ba, sai dai yatsun zargi, sun karkata kan kungiyar Boko Haram, da ta yi kaurin suna wajen kai hare-haren kunar bakin wake da mata manya da kumakanana.

Sama da mutune dubu 20 rigimar mayakan mayakan tarzomar Boko Harma ta salwantar, tun shekara ta 2009 da kungiyar ta fara kaddamar da harehare a arewacin Najeira.