1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Hari da wuka a Jamus ya halaka mutane biyu

Suleiman Babayo AS
October 18, 2022

Mutane biyu sun mutu kana na uku ya samu raunika lokacin da wani mahari ya daba wuka kan mutane a yankin kudu maso yammacin Jamus.

https://p.dw.com/p/4IMry
Garin Ludwigshafen na Jamus bayan harin da wuka da mutane biyu suka mutu
Garin Ludwigshafen na Jamus bayan harin da wukaHoto: Keutz TV-NEWS/dpa/picture alliance

Mutane biyu sun mutu kana na uku ya samu raunika sakamakon hari da wuka a yankin kudu maso yammacin Jamus. 'Yan sanda sun kama maharin bayan bude masa wuta mai shekaru 25 dan kasar Somaliya a garin Ludwigshafen.

A kasar ta Jamus ana samu hare-hare masu nasaba da matsanancin ra'ayi da kuma masu matsalar kwakwalwa, amma zuwa yanzu 'yan sanda ba su bayyana dalilin harin da aka kai a wannan Talata ba.