Hargitsin cikin gida na ci gaba da addabar PDP | Siyasa | DW | 30.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hargitsin cikin gida na ci gaba da addabar PDP

Kasa da kwanaki biyu da gudanar da zaben shugaban kungiyar gwamnoni na PDP a Najeriya, rarrabuwar kawuna da rudani na ci gaba da yin tasiri a lamarin.

Sannu a hankali dai yana kara dumi da daukar hankali, sannu a hankali kuma kowa ya fara gane irin kuka na abokai da abokan adawar sa a cikin jamiyyar PDP da daga dukkan alamu tayi nisa a cikin gwagwarmayar mallakin ruhin ta kuma ke shirin zaben mutumin da zai jagoranci makomar gwamnonin kasar 36.

A al'adance dai ana kallon kungiyar da ta zauna ta kai ga fitar da shugabanni tun daga marigayi umar musa Yar adua ya zuwa ga shugaba jonathan dake ci a yanzu a matsayin kungiya mafi tasiri a cikin fagen siyasar tarrayar Nijeriya

To sai dai kuma daga dukkan alamu ta tafasa tana ma shirin konewa a tsakanin manyan bangarorin dake ja da juna da kuma kellon awayo 48 masu zuwa a matsayin daya daga cikin lokuta mafi tasiri ga burin tabbatar da ikonsu cikin harkokin mulkin kasar ta nigeria.

18.03.2013 DW online Karte Nigeria Kano eng

Taswirar Najeriya

Tuni dai awoyi 72 da suka gabata suka fassara irin zukatan masu goyon bayan kawo karshen ikon gwamna Rotimi Ameachi na jihar Rivers mutumin da ke son sake tsayawa takarar mukamin shugaban kungiyar gwamnonin mutumin kuma da ya kalli dakatar da jirgin saman da yake amfani dashi domin zirga zirga da kuma dakatar da yan majalisar dokokin sa har 27 duk dai daga PDP dakuma fadar gwamantin kasar dake sara tana muanta sanya dafi a cikin raunin.

Fadar kuma da ta fito tace dan kararta na zaman gwamna Ibrahim Shehu na shema dake zaman gwamnan Katsina mutumin kuma da tuni ake rade radin yiwuwar ciccidashi don maye gurbin mataimakin shugaban kasar dake kai yanzu domin taka baya ga shugaba jonathan a zaben na shekara ta 2015.

To sai dai kuma a Murtala Hamman Yero Nyako dake zaman gwamnan ga jihar Adamawa kokari na cin mutuncin wani gwamna da nufin cika burin mulki na shekara ta 2015 dai na zaman babban kuskure a bangare na yan siyasar kasar ta Nijeriya damasu mulkin ta.

Dogaro da Allah don mulki ko kuma kokari na kowa tasa ta fishe shi dai daga dukkan alamu batun na shekara ta 2015 ya dora jamiyyar cikin tsaka mai wuya da ta jima bata kalli irin ta ba.

Abun kuma da wasu ke ganin na iya shafar shi kansa batun mulkin da jammiyyar ta share shekaru har 14 kansa kuma ke fatan wasu 60 masu zuwa a ciki.

President Goodluck Jonathan speaks during the ruling party primary in Abuja, Nigeria, Thursday, Jan. 13, 2011. Delegates of Nigeria's ruling party began voting Thursday night to pick its presidential candidate, choosing between honoring a power-sharing agreement by selecting a Muslim or endorsing the oil-rich nation's current Christian leader. (AP Photo/Sunday Alamba)

Jonathan da Namadi Sambo

Ga dai barazana mafi girma daga bangaren adawar da ya kama hanyar gano baki ga zaren bayan share shekaru yana gwaji yana shan kashi, sannan kuma ga tsanannin rashin tsaro da cin hancin da ya kama hanyar maida kasar wani daji irin na mai karfi sai Allah ya isa, sannan kuma ga sabon rikicin da ko bayan gwamnoni da fadar ta aso rock ya kai ga yin sartse har a cikin jamiyyar da kusan dukkanin shugabanta ke fuskantar kalubalen sahihancin zabensu gaban kotu.

Abun kuma duk acewar bala kaoje dake zaman ma'ajin jamiyyar na kasa ke da ruwa da tsaki da wasu yan kanzagin dake cikin fadar gwamantin kasar ta Aso rock.

Ana dai saran share tsawon daukacin lokacin dake akwai ana taruka da nufin neman mafitar zaben dake zaman zakaran gwajin dafin inda siyasar kasar ke shirin nufa a shekaru biyu masu zuwa.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin