Hare-hare kan cibiyoyin tsaro a Najeriya | Siyasa | DW | 26.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hare-hare kan cibiyoyin tsaro a Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun kai farmaki ofishin rundunar musamman da ake tsare wadanda suka aikata miyagun laifuffuka da ke Abuja, fadar gwamnatin Najeriya.

Rundunar yan sandan Najeriyar dai ta bayyana cewa gungun wasu yan bindiga ne da ba'a san yawansu ba su ka afkawa rundunar musamman ta zarattan yan sandan, inda masu harin su ka dinga harbi da bindigogi da karfe biyu na daren Lahadi. Harin da ya haifar da maida murtani daga 'yan sandan da ma dalilin yunƙurin arcewar fursunoni talatin da ake tsare da su.

To sai dai kakakin rundunar yan sandan Najeriyar Frank Mba ya bayyana cewa an samu nasarar sake kame fursunoni ashirin da biyar daga cikin talatin din da su ka yi yunƙurin guduwa yayinda ake ci gaba da neman sauran guda biyar da su ka arce, haka nan an kame mutane biyu daga cikin wadanda su ka kai harin. Sanin cewar wuri ne da ake tsare da mutanen da ake zargin da aiyyuka na ta'adanci ya sanya tambayar Frank Mba ko irin wannan fususnonin na cikin waɗanda su ka samu arcewa.

Nigeria Anschlag

Ofishin 'yansanda da wani harin ƙunar baƙin wake ya lalata

Ya ce ''ai na yi maka cikakken bayani cewa babu wani daga cikin waɗanda ake zargi da aiyyukan ta'adanci ko wanda mu ke tsare da shi ko ake bincike a kansa daga cikin mutane biyar da su ka arce''.

Irin munanan hare-haren da ake kaiwa a kan wuraren da a zahiri ake masu kalon suna da cikakken tsaro a Najeriya na sanya tunanen inda aka dosa a kan wannan lamari, abinda ya sanya tambayar Dakta Rabe Nasir kwarare a kan tsaron Najeriyar ko me wannan ke nufi ga yanayin tsaron ƙasa da ma al'ummarta.

Dakta Rabe Nasir ya ce ''mu na da matsaloli ƙwarai da gaske a kan gazawar jami'an tsaro a ƙasar nan, wanda ya ke a ko da yakushe na ke fada gazawar akwai dalilai da yawa. Jami'an tsaron nan su mu ka sa ido su taimaka domin a samu nasarar wannan al'amari amma an dabaibaye su da matsaloli da yawa, matsalolin da su ka hada da rashin isasun kudi da na kayan aiki da rashin ƙwarewa, sanna da son zuciya na wasu daga cikin jami'an tsaron. To mu a Najeriya za ka ga cewa babu wanda ya kuɓuta daga cikin wannan al'amari''

Polizeiposten in Nordnigeria

Jami'an tsaro a shingen binciken ababan hawa

To sai dai kakkain rundunar yan sandan Najeriyar Frank Mba na mai bayyana cewar irin yadda aka ɓulowa wannan hari na nuna ƙwarewar aiki a wannan fani.

Ya ce ''ai saboda ƙwarewar aiki da dubarun da su ka nuna ya sanya abin ya tsaya a haka, domin wannan hari ne da aka kai inda su ke ɗauke da bindigogi su ka afkawa wurin. Shi yasa daga cikin mutane ashirin da biyar da aka samu nasarar sa ke kame su koda mutum daya ba'a harba ba''.

Tuni dai aka dauki Karin matakan tsaro a mafi yawan muhimman wurare da ke birnin Abuja da kewaye musamman a wurin da aka kai harin, duk da cewar har zuwa wannan lokaci babu cikakken bayani na zahirin barnar da aka yi a wajen da aka kai harin kuma babu wata ƙungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita : Yahouza Sadissou Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin